Hatsarin Jirgin ruwan Neja: Adadin waɗanda suka mutu ya kai 60

0
1000106026
Spread the love

Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya auku a jihar Neja da ke arewacin Najeriya ya ƙaru zuwa 60.

A baya dai, rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin ruwan wanda ke ɗauke da fasinjoji 90 waɗanda ya ɗauka daga mazaɓar Tugan Sule, da ke yankin ƙaramar hukumar Borgu ta jihar, ya yi hatsari.

Bayan aukuwar hatsarin kuma, a ranar litinin ɗin da ta gabata hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, ta bakin shugabanta, Abdullahi Baba Arah, ta tabbatar da samun gawarwakin mutum 29 daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya rawaito cewa, an ƙara samun gawarwakin mutane inda adadin ya ƙaru zuwa 60.

Kazalika, tun a ranar talata, aka yi jana’izar waɗanda aka sake samun gawarwakinsu kamar yadda addinin muslunci ya tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *