An gudanar da yarjejeniyar zaman lafiya karkashin Operation Safe Corridor a Musawa, Katsina

0
1000109031
Spread the love

An cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin al’ummar Karamar Hukumar Musawa da ‘yan bindiga a karkashin shirin Gwamnatin Jihar Katsina na Operation Safe Corridor.

Wani mai sharhi a fannin tsaro Zagazola Makama ya ruwaito cewa, tattaunawar da aka gudanar a ranar Lahadi a makarantar firamare ta Tashar Mai Alewa da ke karamar hukumar Danmusa, an yi ta ne da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa da sulhu.

Tawagar al’ummar Musawa ta samu jagorancin shugaban karamar hukumar, tare da rakiyar Hakimin Musawa da sauran masu ruwa da tsaki.

A bangaren ‘yan fashin kuwa, wakilansu sun hada da Ummaru Munore da Wada Turawa, wadanda suka shiga ta hannun mai shiga tsakaninsu, Ardo Abdulkarim Yantumaki.

A cewar sanarwar, bangarorin biyu sun amince da inganta zaman lafiya, da tabbatar da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma tabbatar da zaman lafiya da adalci ga kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *