Wata mata mai ciki ta rasa tagwayen cikin ta akan rashin biyan N28,000 a Abuja

0
1000107099
Spread the love

Wani lamari mai ban tausayi ya faru a babban birnin tarayya Abuja, inda wata mata mai juna biyu ta rasa ’yan tagwaye bayan an nemi ta kawo kuɗin haihuwa na ₦28,000 tare da takardar shaida ta asibiti kafin a mata aiki.

Rahotanni sun bayyana cewa matar, wacce ke cikin nakuda, ta kasa samun kuɗin da aka nema yasa ta fara tafiya a ƙasa tana cikin nakuda domin neman mafita, yayin da mijinta ke fama da rashin lafiya.

Wata majiya ta bayyana cewa a hanya wata mutumiyar kirki ta tarar da ita, ta tausaya sannan ta garzaya da ita zuwa cibiyar kiwon lafiyan amma duk da ƙoƙarin da aka yi, tagwayen cikin sun rasa rayukan su sakamakon wahalan nakuda.

Lamarin ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda jama’a ke sukar yadda ake jefa marasa lafiya cikin halin kunci kafin samun kulawa.

Wasu na ganin matsalar ta samo asali ne daga tsadar kiwon lafiya da rashin kayan aiki a asibitocin Najeriya, lamarin da ke jefa mata masu ciki cikin haɗari.

Lamarin ya sake haifar da tattaunawa kan tasirin matsin tattalin arziki da tsarin kiwon lafiya a Najeriya, musamman kan yadda rashin kulawa ke jefa rayukan mata da jarirai cikin haɗari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *