An ba ma’aikatan VOA sama da 500 takardar sallama daga aiki

0
1000105515
Spread the love

Gwamnatin Trump ta dauki matakin korar sauran ma’aikatan kafar yada labarai ta gwamnatin kasar Muryar Amurka wato kafar VOA.

An aika wa ma’aikata fiye da 500 takardar sallama daga aiki a kafar da yaɗa labarai.

Shugabar riko ta kafar yada labaran, Kari Lake, ta sanar da wannan mataki na rage ma’aikatan a shafinta a kafar sada zumuntarta.

Ta ce matakin zai taimaka wadanda aka zaba damar tafiyar da gwamnati da rage kudin harajin da ake kashewa, duk da a kwai yiwuwar za a kalubalanci wannan mataki a kotu.

A lokacin yakin duniya na biyu ne aka samar da kafar yada labaran ta VOA domin dakile farfagandar da ake yada wa akan ‘yan Nazi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *