Gwamnatin Sokoto ta ware wa kowane masallacin Juma’a naira 300,000 zuwa 500,000 a wata

Gwamnatin jihar Sokota ta ce za ta fara ware wa masallatan Juma’a na jihar wasu kuɗaɗe duk wata domin gudanar da ayyukansu, sannan ta ce tana ware wa limaman masallatan da na’ibansu da ladanai alawus duk wata.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar, Abubakar Bawa ya fitar, inda ya ce gwmnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin haɓaka karatun Alƙu’ani da ilimin addini a tsakanin yaran jihar masu tasowa.
Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana haka a ranar Asabar a wajen yayen ɗalibai 111 da suka haddace Ƙur’ani a makarantar gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi da ke Sokoto, inda ya ƙara da cewa alawus ɗin zai taimaka wajen ba malaman addinin damar nazari da ci gaba da karantar da addini.
