An kammala taron Gwamnonin Arewa maso Gabas a Jalingo

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) da ta ƙunshi gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe, ta gudanar da taronta na 12 a Jalingo, jihar Taraba,inda gwamnonin su ka yi bitar lamuran da suka jibanci tsaro, zamantakewa da tattalin arziki na yankin.

Gwamnonin a karshe sun sanar da cimma wasu daga cikin muradu kamar da haka:
Ana samu nasarori a kan yaki da ta’addanci a wasu wurarren duk da barzana da kungiyoyin ke yi,ga matsallar jin kai a wasu yankuna.

Gwamnonin sun yi la’akari da hasashen da hukumomi masu sahihanci suka yi kan hadarin yanayi da bala’in ambaliya da ke tafe a wasu yankuna,don haka suka yi kira da a dauki matakan tunkarar ambaliyar ruwa da kuma wayar da kan mazauna yankunan da ke gabar ruwan.
Haka kuma ta bukaci goyon bayan gwamnatin tarayya da hukumar bunkasa yankuna wajen samarwa jama’a ababen more rayuwa domin sake gina ababen more rayuwa da suka lalace musamman gadoji da ambaliyar ruwa ta shafa.

Ƙungiyar Gwamnonin ta bayyana adawa da tsarin karin kudin kayan aikin noma wanda zai iya haifar da mummunan sakamako a kan amfanin gona a shekara mai zuwa.
Don kawar da matsalar abinci da ke gabatowa, tana buƙatar ƙarin tallafi ga manoma da ƙwaƙƙwaran shiri don noman rani.
Gwamnonin sun amince da gudanar da bikin baje kolin kasuwanci na arewa maso gabas tare da hadin gwiwar NECCIMA, a Maiduguri, jihar Borno, Disamba, 2025.
