An nada Sanusi Mika’ilu Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru

0
1000099535
Spread the love

Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris ya amince da nadin Sanusi Mika’ilu Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru.

Da yake gabatar da wasikar ga sabon Sarkin ranar Alhamis a garin Zuru, Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Garba Umar Dutsin-Mari ya ce an aiwatar da nadin ne bisa shawarar kwamitin zaben.

Ya ce daga cikin ‘yan takara uku da suka nemi wannan mukami da kwamitin zaben Masarautar Zuru ya tantance, Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami ya samu kuri’u mafi yawa da ya dace ya hau kan karagar mulki.

Nadin sabon Sarkin ya biyo bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Sani Sami Gomo II, wanda ya rasu a ranar 16 ga watan Agusta, 2025 a wani asibitin Landan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *