Har yanzu akwai rashin tabbas dangane da makomar Manchester United

Rashin nasarar da Manchester United ta yi a hannun Grimsby Town ya jawo cecekuce a faɗin duniya bayan doke ta 12-11 a bugun finareti ranar Laraba da dare a kofin Carabao.
Har yanzu tawagar ta Ruben Amorim ba ta ci wasa ba a gasar bana, abin da ya ƙara jefa shi cikin matsi.
Magoya bayan Man United sun tsammaci abin kirki a karawar da suka yi da ƙungiyar da ke buga gasa matsayi na uku a Ingila bayan kashe kusan fan miliyan 200 wajen cefane.
Amorim ya fi kowane mai horarwa na Man United yawan kaso na rashin nasara tun bayan tafiyar koci Alex Ferguson.
Kocin ɗan ƙasar Portugal ya ci wasa 16, da canjaras 12, da kuma rashin nasara 17 cikin wasa 45 da ya ja ragama zuwa yanzu.
Hatta Ralf Rangnick, wanda ya jagoranci ƙungiyar tsakanin watan Disamban 2021 zuwa Mayun 2022, ya fi samun kaso mai yawa na nasara da kashi 38 cikin 100.
