Tsohon Kwanturola Janar na Kwastam Mustapha ya rasu

Tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Ahmed Aliyu Mustapha, ya rasu.
Mustapha ya rike mukamin Kwanturola Janar daga 1999 zuwa 2003.
Ya yi ritaya daga aiki a cikin Disamba 2003, bayan fiye da shekaru talatin na aiki.
Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ne ya tabbatar da rasuwarsa a ranar Alhamis a wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.
Mustapha, wanda dan uwa ne ga Lamidon Adamawa, Alhaji Dr. Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, shi ma ya rike sarautar Sardaunan Adamawa.
