Gwamnonin PDP sun hallara a jihar Zamfara domin gudanar da taron su.

Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun hallara a birnin Gusau na jihar Zamfara domin yin wani taron tattaunawa.
Suna gudanar da taron ne a matsayin sharar fage kafin taron kwamatin gudanarwa mai muhimmanci da za su yi ranar Litinin mai zuwa.

Ministan Abuja Nyesom Wike – wanda har yanzu yake iƙirarin zama ɗan jam’iyyar duk da kasancewarsa a gwamnatin APC mai mulki – ya soki taron da za a yi a jihar Oyo, inda ya ci alwashin hana gudanar da shi.
Gwamna Dauda Lawal ne ke karɓar baƙuncin gwamnonin tara daga sassan Najeriya a yau Asabar.
