‘Ba mu cire arewa maso yamma cikin waɗanda za su ci gajiyar wankin ƙoda ba’

Ma’aikatar lafiya ta tarayya ta musanta rahotanni da ke cewa babu marasa lafiya daga arewa maso yamma cikin waɗanda za su ci gajiyar shirin rage farashin wankin ƙoda da gwamnatin ƙasar ta amince da shi ba.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X, ta ce labarin ba shi da kamshin gaskiya.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne dai ya amince da rage farashin wankin ƙoda a manyan asibitocin tarayya a faɗin ƙasar.
Karkashin tsarin, za a rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000.
Shirin wanda aka ɓullo da shi karkashin shirin Renewed Hope na kyautata rayuwar ƴan Najeriya, yana cikin ƙoƙari da gwamnatin tarayya ke yi wajen rage wa masu fama da cutukan da suka jiɓanci ƙoda raɗaɗi.
An fara shirin ne a manyan asibitocin tarayya guda 11 a faɗin ƙasar.
Asibitocin sun haɗa da:
Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, a jihar Kano
Asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, a jihar Borno
Asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, a jihar Bauchi
Asibitin koyarwa na jami’ar Jos, a jihar Filato
Babban asibitin ƙasa na Abuja
Asibitin gwamnati tarayya a Ebute Metta, jihar Legas
Babban asibitin koyarwa a Ibadan, a jihar Oyo
Asibitin koyarwa na jami’ar Benin, a jihar Edo
Asibitin gwamnatin tarayya a Yenagoa, jihar Bayelsa
Asibitin koyarwa a Owerri, jihar Imo
Asibitin gwamnatin tarayya a Abakaliki, jihar Ebonyi
Sanarwar ma’aikatar ta lafiya ta ƙara da cewa za a faɗaɗa shirin domin ya kai ga ƙarin asibitocin gwamnatin tarayya a faɗin ƙasar, inda ta ce babu ɗan Najeriya da za a bari a baya wajen cin wannan gajiya.
“Gwamnatin tarayya na ci gaba da hobbasa wajen ganin ta rage barazanar kamuwa da cutuka da kuma kare lafiyar duka ƴan Najeriya,” in ji ma’aikatar.
