Ƴan Najeriya miliyan 31 na fuskantar matsalar ƙarancin abinci – MDD

Ofishin hukumar kula da jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna damuwa kan ƙaruwar yunwa da talauci da kuma rashin tsaro a Najeriya, inda ta yi kiyasin cewa ƴan ƙasar miliyan 31 na fama da matsalar ƙarancin abinci.
Hukumar ta ce akwai sama da yara miliyan goma ƴan ƙasa da shekara biyar da ke fama da rashin abinci mai gina jiki.
Bayanin haka ya fito ne a taron da gwamnatin tarayya da hukumar suka gudanar yayin bikin ranar Jin-Ƙai ta Duniya na 2025, wanda aka gudanar ranar Talata a Abuja, mai taken “ƙarfafa haɗin gwiwa a duniya da kuma tallafawa al’ummomi”.
Hukumar ta ce ya kamata a ɗauki matakai cikin gaggawa domin rage barazanar ƙaruwar matsalar.
Jami’in hukumar ta jin-ƙai a Najeriya, Mohamed Fall, ya bayyana cewa bikin ranar ta bana ya zo ne a daidai lokacin da ake samun raguwar bayar da taimakon jin-ƙai ga mabuƙata a duniya.
“Buƙatar jin-ƙai na ƙaruwa a Najeriya, sakamakon matsalar ƙarancin abinci da rashin abinci mai gina jiki. Yanzu akwai ƴan Najeriya miliyan 31 da ke fama da matsalar ta ƙarancin abinci,” in ji shi
