Shugaba Tinubu ya nada sabbin shugabannin gudanarwa na NTA

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya nada Rotimi Richard Pedro, wanda ya fito daga Legas, (Kudu maso Yamma) a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya.
Shugaban ya kuma nada Karimah Bello daga Katsina, (Arewa-maso-Yamma) a matsayin babbar daraktar kasuwanci.
Sauran mambobin tawagar gudanarwar su ne Stella Din daga Jihar Filato, (Arewa ta Tsakiya), a matsayin sabuwar babbar daraktar labarai, yayin da Sophia Issa Mohammed daga Jihar Adamawa, (Arewa-maso-Gabas) ta zama Manajan Darakta na NTA Enterprises Limited.
Nadin nasu ya fara aiki nan take bisa ga sanarwan da aka wallafa a shafin X na fadan Shugaban kasa.
