Sayan kuri’u babbar barazana ce ga dimokraɗiyyar Najeriya – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi ya yi gargaɗi kan masu sayan kuri’u, inda ya kwatanta hakan da cewa barazana ce ga dimokraɗiyyar Najeriya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce waɗanda ke sayan kuri’u suna so ne kawai su kai ga duƙiyar al’umma domin yin almundahana.
A cewarsa, kuɗaɗen da aka ware don gina makarantu da asibitoci da kuma hanyoyi na karewa da shiga aljihun ƴan siyasa masu sayan kuri’u da zarar sun shiga ofis.
“Waɗannan mutane ba shugabanni bane, masu satar duƙiyar ƙasa ne.
Ɗabi’unsu na yi wa al’umma lahani da kawo cikas wajen samar da cigaba,” kamar yadda Obi ya rubuta.
Tsohon gwamnan jihar Anamba ya kuma soki masu kaɗa kuri’u waɗanda ke sayar da kuri’unsu don kuɗi, inda ya ce suna sayar da makomarsu ce.
“Idan ka sayar da kuri’arka, tamkar kana sayar da makarantun da ya kamata ƴaƴanka su je ne da asibitoci da ya kamata su ceci rayuka da kuma ayyuka da za su inganta iyalai da fitar da su daga kangin talauci,” a cewar Obi.
Ya buƙaci ƴan Najeriya su daina sayar da kuri’unsu don zaɓar ƴan siyasar da za su kawo cigaba a ƙasar.
