M23 sun kashe aƙalla fararen hula 140 a Kongo – HRW

0
1000081823
Spread the love

Ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam ta Human Rights Watch ta ce ta kammala tattara shaidu da ke tabbatar da cewa ‘yan tawayen M23 na Kongo sun kashe aƙalla fararen hula 140 a watan da ya gabata, galibi ‘yan ƙabilar hutu da suka haɗa maza da mata da kuma yara.

Kazamin kisan da ake zarginsu da aikata wa a Virunga, shi ne mafi muni da ‘yan tawayen suka yi a cikin sama da shekara uku, duk da ƙoƙarin da ake yi na ganin an samar da zaman lafiya a rikicin da ake yi da su a gabashin Congo.

Ƴan tawayen M23 sun musanta wannan rahoto.

MDD da wasu majiyoyi daga sojojin Rwanda sun tabbatar da cewa akwai hannun Rwanda a aikata kisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *