A shirye muke wajen tabbatar da tsaro a zaben cike gurbi na Ganye – ‘Yan Sandan Adamawa.

0
1000070956
Spread the love

Rundunar ‘Yan Sandan Adamawa sun bayyana cewar a shirye suke domin tabbatar da bin doka da oda a zaben cike gurbi da za’a gudanar a karamar hukumar Ganye.

A cikin wata sanarwan da kakakin yan sandan Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya bayyana cewa a bisa umarnin Mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya na tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta karbi bakuncin AIG Taiwo O. Adeleke, AIG mai kula da sa ido kan zaben mazabar Ganye da aka shirya gudanarwa ranar Asabar 16 ga watan Agusta, 2025.

AIG Taiwo tare da Komishinan Yan Sanda CP Moses Ottah da ACP Husseini Yelwa, sun gana da hafsoshi da jami’an rundunar domin duba dabarun gudanar da aiki da nufin samun nasarar zabe cikin kwanciyar hankali.

Ya bukaci dukkan ma’aikata da su maida hankali wajen aikin su da kuma inganta muamala da fararen hula a yayin da suke mu’amala da jama’a, yana mai jaddada hakkin ‘yan sanda na samar da tsaro kafin zabe, lokacin da kuma bayan zabe.

Tun da farko, CP Dankombo Morris ya yi maraba da AIG tare da yi masa bayani game da shirye-shiryen rundunar, ciki har da shirye-shiryen turawa da kuma tsara matakan da suka dace don tabbatar da tsaron lafiyar masu zabe, jami’an INEC, da kayan zabe.

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar wa al’ummar jihar kan jajircewarta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da bin doka da oda, da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro, tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu da ake zargi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *