Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara

Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara a faɗin Najeriya.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan taron majalisar zartarswa ta ƙasa da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja.
Ya ce jami’o’in da aka amince da su sun haɗa da:
- Jami’ar Tazkiyah da ke jihar Kaduna
- Jami’ar Leadership da ke babbar birinin tarayya, Abuja
- Jami’ar Jimoh Babalola a jihar Kwara
- Jami’ar Bridget, Mbaise a jihar Imo
- Jami’ar Greenland da ke jihar Jigawa
- Jami’ar JEFAP a jihar Neja
- Jami’ar Azione Verde da ke jihar Imo
- Jami’ar Unique Open a Jihar Legas
- Jami’ar American Open da ke Jihar Ogun
Alausa ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaji buƙatu 551 na kafa sababbin jami’o’i, inda aka saka tsauraran ka’idojin tantancewa kafin amincewa da su.
Ƙa’idojin tantancewar ta saka buƙatun kafa sabbin jami’o’in zuwa guda 79 wanda kuma daga cikinsu ne aka amince da kafa guda tara a ranar Laraba.
Ministan ya ƙara da cewa da dama daga cikin jami’o’in da aka amince da su suna jiran samun izinin aiki sama da shekaru shida, duk da cewa masu hannun jari sun riga sun gina harabar makaranta tare da zuba biliyoyin naira a ciki.
“Rashin inganci a cikin hukumar NUC ne ya jawo jinkirin amincewa da buƙatun. Mun aiwatar da wasu gyare-gyare don sauƙaka tsarin.”
Ministan ya kuma ƙoƙa da cewa ana ɓarnar kuɗi ne kawai wajen kafa jami’o’i saboda wasu ba su ma da isassun ababen koyarwa.
“Alal misali, akwai wata jami’a a ƙasar nan da ke da ɗalibai ba ba su haura 800 ba da malamai 1,200. Haka lamarin yake a yawancin jami’o’i a ƙasar nan,” in ji Alausa.
