Taraba: Matasan Jukun sun yi Allah-wadai da kisan da wasu makiyaya suka yi wa manomi

0
1000067717
Spread the love

Kungiyar matasan ‘Kabilan Jukun, ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa daya daga cikin mambobinta, Nwubu Gani Pujen, a karamar hukumar Wukari ta jihar Taraba.

Kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin wani abin takaici da rashin hankali.

Lamarin da ke ci gaba da haifar da tashin hankali, ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, 10 ga Agusta, 2025.

Kungiyar ta yi Allah wadai da lamarin a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugabanta, Mista Audu Danjuma.

Kungiyar ta JYCDA ta kuma yi zargin cewa an kai wa Nwubu hari tare da kashe shi bayan gano dimbin barnatar da gonarsa da ake zargin Fulani makiyaya ne suka yi.

Kungiyar ta yi kira ga jami’an tsaro da kungiyoyin sa ido na cikin gida da su gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da sun fuskanci kwakkwaran hukunci, tana mai jaddada cewa dole ne a yi adalci ba tare da tsoro ko nuna son kai ba don dakile hare-haren nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *