Shirin Tuntuba na harkokin noma da samar da abinci mai gina jiki, wato Sahel Consulting Agriculture and Nutrition Limited, ta horas da manoma 300 a jihar Adamawa don Bunkasa harkokin Noma.

Shirin Tuntuba na harkokin noma da samar da abinci mai gina jiki Sahel, ta horas da manoma 300 a jihar Adamawa kan hasashen yanayi na watan Agusta da Satumba da kuma watan Oktoba kan lokacin da ake tsamanin ruwa da kuma rigakafin ambaliyar ruwa da ake fargaban sake samun sa a jahar.
Baya ga haka kuma sun kafa kwamitin da zasu sa ido kan kula da yanayi da kuma isar da dukkan bayanai ga jama’a.
Wannan horaswa ya zo ne makonin biyu bayan iftila’i ambaliyar ruwa da ya faru a jahar tare da halaka mutane 26.
