Gwamnan Kano ya sallami masu taimaka masa guda biyu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sallamar masu taimaka masa guda biyu bisa laifuffuka daban-daban, sannan aka wanke guda ɗaya bayan kwamitocin bincike sun gabatar da rahoton binciken su.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Musa Tank Muhammad ya fitar.
Sanarwar ta ce gwamnan ya amince da sallamar Abubakar Umar Sharada, babban mai taimaka wa gwamna kan tattara jama’a bayan kwamitin binciken ya gano shi ne ya kitsa yadda aka yi belin wanda ake zargi da fataucin miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Haka kuma gwamnan ya amince da sallamar Tasiu Al’amin Roba bayan kwamitin bincike ya tabbatar da hannunsa a kwana da kayan tallafin a rumbun gwamnati na Sharaɗa, wanda kuma tuni aka gabatar da shi a gaban shari’a.
Sai dai kuma gwamnatin ta amince da rahoton kwamitin bincike da ya wanke Musa Ado Tsamiya mai ba gwamnan shawara kan magudanan ruwa.
Gwamna Abba ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin amana ba, sannan ya yi kira ga dukkan jami’an gwamnatin da su ƙara ƙaimi wajen riƙe gaskiya da amana.
