,’Yan sanda sun saki Omoyele Sowore bayan kama shi na sa’o’i 48.

0
1000060786
Spread the love

Rundunar ƴansandan Najeriya ta saki ɗangwagwarmaya, Omoyele Sowore bayan kiraye-kirayen da aka yi na buƙatar a sake shi.

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasan ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya alaƙanta sakin nasa da nasarar kiraye-kiran sakin nasa da aka yi.

Ya rubuta cewa, “Ƴansandan Najeriya sun amsa buƙatar ƴan gwagwarmaya. Yanzu haka an sake ni daga tsare ni da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.

“Sai dai ya ce babu wani abin farin ciki a sakin, “amma ina godiya gare ku da jajircewar da kuka yi ba tare da gajiyawa ba

.”Tun da farko, wasu matasa ne suka gudanar da zanga-zanga a Abuja da Legas da wasu biranen ƙasar, inda suka buƙaci ƴansanda su sake shi ba tare da ɓata lokaci ba.

A ranar Laraba ne da ƴansanda suka gayyace shi domin amsa wasu tambayoyi, sannan rundunar ta sanar da cewa tana tsare da shi bayan ya ƙi amsa tambayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *