Ya kamata a dakatar da Wike da Ortom da Ikpeazu daga PDP – Lamido

0
1000060783
Spread the love

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi kira da a kora Ministan Abuja, Nyesom Wike da tsohon Gwamnan Benue Samuel Ortom da tsohon Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu da sauran ƴan PDP da suka yi mata unguwa da kan zabo a zaɓen 2023 daga jam’iyyar.

Lamido ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar Channels a shirinta na Politics Today a ranar Juma’a, inda ya ce dole uwar jam’iyyar ta ɗauki matakin ba sani ba sabo.

“Duk irin waɗannan mambobin jam’iyyar da suka mata ungulu da kan zabo irin su Wike da su Ikpeazu da Ortom da sauran su da suka fito fili suka yi adawa da jam’iyyar a zaɓen 2023, sannan kuma suka ce APC za su yi wa aiki a zaɓen 2027 ya kamata a kore su daga jam’iyyar.”

Haka kuma Lamido ya ce zai janye jiki daga taron kwamitin amintattu na PDP har sai an ɗauki matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *