Jam’iyyun hamayya a Kamaru sun soki matakin kotu na hana Kamto takara.

Jam’iyyun hamayya a Kamaru sun soki matakin Kotun Tsarin Mulkin ƙasa na dakatar da takarar jagoran ƴan adawar ƙasar, Maurice Kamto a babban zaɓen ƙasar na watan Oktoba.
Jami’an Jam’iyyar MRC wadda Maurice Kamto ya kafa ta soki matakin kotun, kamar yadda gidan redion RFI ya ruwaito.
Jam’iyyar MANIDEM ta zaɓi Kamto ya yi mata takara a zaɓen da ke tafe sai dai hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa ɗantakara Dieudonne Yegba shi ne halastaccen ɗantakarar jam’iyyar ta MANIDEM.
Kotun ta kuma soke takarar wani ɗan takarar da hukumar zaɓen ƙasar ta amince da shi, hakan ya kuma ƙara rage yawan ƴan takarar da za su fafata a zaɓen na Oktoba zuwa 12, ciki har da shugaba mai ci, Paul Biya mai shekara 92 a duniya.
