Ƴanbindiga sun sace mutum 150 cikin kwana huɗu a Zamfara

0
20250421_095436
Spread the love

Rahotonnin daga jihar Zamfara a yankin arewa maso yammcin Najeriya na cewa ƴanbindiga sun sace mutum 150 a jerin hare-haren da suka kai wasu garuruwan jihar cikin kwanaki huɗu da suka gabata.

Kakakin gwamnatin jihar Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa ya tabbatar wa da BBC kai hare-haren, kodayake bai yarda ko musanta adadin ba, sai dai ya ce gwamnati na ƙoƙarin kuɓutar da mutanen.

Mazauna garuruwan sun ce ƴanbindigar ɗauke da muggan makamai sun kai jerin hare-hare cikin kwana huɗu a ƙauyukan Sabon Garin Damri da Dakko Butsa (da ke iyaka da Sokoto), da Tungar Abdu Dogo da Tungar Sarkin Daji da Sadeda kuma Tungar Labi.

Ƴanbindigar na bin dare ko lokacin ruwan sama domin auka wa ƙauyukan a lokacin da mutane ke tsaka da barci.

Bayanai sun ce rashin kyawun titunan jihar na taimaka wa ƴanbindigar, inda jami’an tsaro ke fuskantar ƙalubale wajen zuwa wuraren da ƴanbindigar ke cin karensu babu babbaka a kan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *