
An zabi tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na kasar Ibadan.
Majalisar masarautar Olubadan ta zabi Ladoja a ranar Litinin, yayin wani taro a fadar Olubadan da ke Oke-Aremo, karamar hukumar Ibadan ta Arewa a jihar Oyo.
Balogun Olubadan na Ibadanland, Oba Tajudeen Ajibola ne ya jagoranci taron.
Da yake magana, Ajibola ya ce, “mu (mambobin majalisar Olubadan) duk mun sanya hannu kuma muka zabi Oba Rashidi Ladoja a matsayin sabon Olubadan na Ibadanland.
“Za mu mika kudurorin taron mu ga gwamnan mu, Seyi Makinde, yanzu zai zabi ranar da zai gabatar da kundin daftarin kama aiki a matsayin sabon Olubadan.
