Kungiyar ‘yan kabilar Igbo ta bukaci jihohin kudu maso gabas da su hana kiwo a yankin.

0
1000051780
Spread the love

Wata kungiya a karkashin kungiyar Igbo National Union Worldwide, INU-W, ta bukaci daukacin Majalisun Dokokin Jihohi a shiyyar Kudu maso Gabas da su fitar da dokar hana kiwo a fili domin magance matsalar hare-haren makiyaya a yankin.

Kungiyar ta kuma yi kira ga al’ummar yankin da su samar da kayan aiki ga ‘yan sa-kai domin kare filayen noma da kuma kawo karshen kashe-kashen da ake yi da kuma yi wa mata fyade.

INU-W ta bayyana cewa abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun tabbatar da cewa ayyukan makiyayan sun fi karfin hukumomin tsaro, domin ba za su iya kama ko gurfanar da ko da makiyayi daya dauke da makami ba.

Shugabar kungiyar ta kasa, Ngozi Ogbomor, da Sakatariyar gudanarwar ta, Austin Mary Ndukwu ne suka yi wannan kiran a wata sanarwa da suka rabawa manema labarai.

Kungiyar ta koka da abin da ta bayyana a matsayin rashin kakkausar suka da tauye hakkin dan adam da makiyaya ke yi a jihohin Gabas biyar da ma sauran su.

A cikin sanarwar da ta fitar, INU-W ta bayar da shawarar cewa, matakin da ya dace na dakatar da kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi a matsayin makiyaya, shi ne mutanen yankin su hada karfi da karfe domin dakile ‘yan ta’adda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *