An kammala taron G20 a Afirka ta Kudu

An kammala taron ƙungiyar G20 ta ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki da aka gudanar a Birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Shugaban Afirka ta Kudu, mai masaukin baƙi, Cyril Ramaphosa ya ce shugabannin ƙungiyar sun sake nanata jaddada ƙudirin ”aiki tare”.
An amince da ƙudirin magance sauyin yanayi, duk kuwa da adawa da hakan da Amurka ta nuna ta hanyar ƙaurace wa taron.
Fadar White House ta zargi gwamnatin Afirka ta Kudu da mayar da shugabancin G20 makamin yaƙi, tana mai cewa za ta gyara hakan a shekara mai zuwa lokacin da Amurka za ta karɓi shugabancin ƙungiyar, wanda na karɓa-karɓa ne.
Amurka ta ƙaurace wa taron ne bayan da Shugaba Trump ya yi iƙirari ”maras hujja” cewa Afirka ta Kudu na muzguna wa tsiraru fararen fata a ƙasar.
