Na saci Indomie na rarraba wa ‘Yan matana 3 – Cewar wani matashi.

0
1000312380
Spread the love

An yanke wa wani matashi mai shekaru 24 mai suna Usama Abdullahi hukuncin yiwa al’umma hidima na yan wasu lokaci a karamar hukumar Shelleng, jihar Adamawa saboda sata.

An yanke wa Usama, wanda ke aiki a wani wurin wanke motoci a Shelleng, hukuncin ne bayan sake duba hukuncin daurin shekaru 2 da aka yi a gidan yari a karamar hukumar.

Kwamitin Kula da Kurkukun Jihar Adamawa ya sake duba hukuncin daurin da aka yanke masa, wanda Babban Alkalin Jihar Adamawa, Justice Hafsat Abdulrahman, ta jagoranta.

Alkali Hafsat, ta sake duba hukuncin da aka yanke masa lokacin da kwamitinta ya ziyarci gidan kurkukun dake Shelleng a ranar Laraba saboda rage cunkoson gidajen yari.

Ta sake duba hukuncin daurin da aka yanke masa daga shekaru 2 zuwa hidimar al’umma.Yayin da ya bayyana a gaban kwamitin, wanda ake tuhuma ya bayyana cewa ya saci fakitin taliya ne ya raba wa ‘yan matan sa 3 kuma ya tsere zuwa Shani inda aka kama shi.

Ya yi nadama cewa tun lokacin da ya shiga a gidan yari babu daya daga cikin matan da ta ziyarce shi, yana mai cewa zai kawo karshen dangantakar bayan ya sake samun ‘yancinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *