Za muyi duk abinda ya kamata wajen ceto ƴan matan sakandaren Kebbi – Shettima

Gwamnatin Najeriya ta bayyana batun ceto ɗalibai 25 da yan ta’adda suka sace a Makarantar mata ta Maga a ƙaramar hukumar Danko Wasagu da ke jihar Kebbi, a matsayin aikin da ba za ta huta ba har sai an kuɓutar da ɗaliban.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinibu ne ya bayyana haka a ziyarar jaje da tawagar gwamnatin ta kai, a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shetima.
Ɗaliban dai na bacci ne ƴan ta’addan suka kutsa ɗakunan kwanansu, kuma suka yi garkuwa da 25 daga cikinsu.
