‘Yansandan Kebbi sun ceto mutane bayan kashe ɗanfashi

Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Kebbi ta ce ta kashe ɗanfashi ɗaya ciki takwas da suka shiga gidan wani mutum a ƙaramar hukumar Maiyama.
Wata sanarwa da kakakin rundunar CSP Nafiu Abdullahi ya fitar ta ce an sace mutum biyu, Muhafi Sani da Shamsiya Aliyu, yayin harin da ‘yanbindigar suka kai ranar Talata.
CSP Nafiu ya ce bayan sun samu rahoton faruwar lamarin ne suka bi sawun maharan ƙarƙshin jagorancin DPO na Maiyama a tawagar da ta ƙunshi ‘yansanda da ‘yan sa-kai.
“Sakamakon haka aka kashe ɗaya daga cikin ‘yanfashin tare da ƙwace bindigarsa harba-ruga da kuma ƙunshin harsashi ɗaya,” in ji shi.
Ta ƙara da cewa wasu ‘yanbindigar sun far wa garin Giron Masa na ƙaramar hukumar Shanga, inda suka sace mutum biyu nan ma.
“Yayin fafatawa da ‘yanbindigar, masu garkuwar sun gudu cikin daji da raunuka kuma suka bar mutanen da suka kama.”
