Nijar ta horas ta matasa don yaƙi da ƴan bindigar da suke tsallaka wa ƙasar daga Najeriya

0
1000283118
Spread the love

Kwararar ƴan bindiga daga Najeriya zuwa yankunan Madarunfa da Gidan Runji a Jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, ya sa hukumomin wannan yanki ɗaukar Matasa 300 aikin soja da nufin taimaka wa Jami’an tsaro tabbatar da zaman lafiya.

Sulhun da ƴan bindigar suka yi a wasu yankuna na Jihar Katsina ya sa sun taƙaita garkuwa da mutane da satar dabbobi a can, lamarin da ya sanya suka karkata akalar kai hare-haren su zuwa Nijar ɗin.

Bayaga waɗannan matasa, akwai kuma wasu garuruwa da dama da ke kan iyakar ƙasar da aka horas da mutanensu akan dubarun kare kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *