An kammala kilomita 39 a titin Abuja-Kaduna-Kano – Gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta ce an kammala kilomita 39 a ɓangarori daban-daban na titin Abuja–Kaduna–Kano da ake ci gaba da yi.
Ƙaramin ministan ayyuka na Najeriya Barista Bello Goronyo ne ya bayyana haka, inda ya ce gwamnatin ƙasar na sa ido sosai kan yadda kamfanin da ke kwangilar, Infiouest International Limited ke gudanar a aikin domin tabbatar da an kammala sashe na 1 na aikin titin kafin watan Afrilun shekarar 2026.
Ya ce zuwa yanzu an buɗe sababbin ɓangarori guda takwas domin aikin ya ƙara sauri, inda ya ce suna da tabbacin titin zai yi ƙarkon da zai kai shekara 50 ana amfani da shi.
“Gwamnatin Bola Tinubu ba gina tituna kaɗai take yi ba, tana ma yunƙurin tabbatar da titunan suna da inganci da ƙarko. Burinsa shi ne shugabannin da za su nan gaba su mayar da hankali kan wasu ayyukan daban, ba gyare-gyaren tituna ba,” in ji Goronyo, kamar yada jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ministan ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya bisa sakin kuɗi isassu domin tabbatar da aikin na tafiya kamar yada ake so.
