Dole PDP ta bayar da gudunmawa don ceto Najeriya – Damagum

0
1000271776
Spread the love

Shugaban babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, Amb. Umar Iliya Damagum ya hori jagororin jam’iyyar su ɗauki gabarar abin da ya kira ceto Najeriya.

Yayin da yake jawabi a wani taron gaggawa da kwamitin amintattun jam’iyyar ya shirya a gidan saukar baƙi na gwamnatin jihar Bauchi da ke Abuja, Damagum ya ce a matsayinta na jam’iyyar hamayya PDP na da rawar da za ta taka.

Cikin waɗanda suka halarci taron har da mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin kudancin ƙasar, Taofeek Arapaja da mai riƙon ƙwaryar muƙamin sakataren jam’iyyar na ƙasa, Koshedo Setonji da tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi da tsohon ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

An gudanar da taron ne da nufin kammala duka wasu shirye-shirye domin tunkarar babban taron jam’iyyar na ƙasa da za a gudanar a Ibadan a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Babban taron dai ya riƙa fuskantar tarnaƙi bayan da a makon da ya gabata wata kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar daga ci gaba da taron.

To sai dai a ranar Talata babbar kotun jihar Oyo ta bayar da wani umarnin gudanar da taron, tare da bai wa hukumar zaɓen ƙasar umarnin sanya idanu kan taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *