Gumi ya buƙaci Najeriya ta yanke alaƙa da Amurka

Fitaccen malamin Addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya ɗauki tsattsauran mataki kan Amurka saboda barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya soki barazanar Trump ɗin da cewa cin zarafi ne da keta alfarmar Najeriya.
“Barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya da Trump ya yi, tsantsar raini ne ga hukumomin Najeriya, amma za mu iya dakatar da shi,” kamar yadda ya wallafa.
Sheikh Gumi ya shawarci gwamnatin Najeriya ta gayaci jakadan Amurka domin ta buƙaci Amurka ta janye barazanar, yana mai cewa ƙin yin hakan zai iya haifar da lalacewar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
