Trump na yunƙurin ƙaddamar da yaƙi a ƙasarmu – Venezuela

0
1000260398
Spread the love

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya sake zargin Amurka da kokarin kaddamar da yaki a kasarsa – a yayin da sojojin Amurka ke cikin shiri a yankin Caribbean.

Mr Maduro ya ce Washinton na son hambarar da gwamnatinsa ne domin kwashe arzikin man kasar.

Shugaba Trump da sakararen harakokin wajensa Marco Rubio sun musanta rahotannin cewa Amurka na shirin kadamar da hare-hare kan Venezuela.

Gwamnatin Trump ta nace cewa an girke sojoji ne domin yaki da masu safarar miyagun kwayoyi – amma ta zargi Mr Maduro a matsayin shugaban masu fataucin miyagun kwayoyi kuma Amurka ba ta amince da shi ba a matsayin halastacen shugaban Venezuela

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *