Ghana ta tilasta amfani da harshen uwa wajen ƙoyar da dalibai a makarantun ƙasar

Gwamnatin Ghana ta ce daga yanzu dole ne dukkanin malamai su yinƙa amfani da harshen uwa, wajen ƙoyar da dalibai a makarantun ƙasar.
Wannan ne dai karo ya farko da harshen Ingilishi, da aka kwashe tsawon shekaru ana amfani da shi wajen koyarwa a Ghana, ya fuskanci koma baya.
Ministan Ilimin ƙasar Haruna Iddrisu ne ya sanar da wannan mataki, wanda ya bayyana a matsayin mai muhimmanci wajen inganta harkar koyarwa da kuma kare martabar al’adun ƙasar ta Ghana.
