2027: Zan goyi bayan Atiku ya zama shugaban kasa a kan Tinubu, ba zan iya shiga APC ba – Tambuwal

Sanatan Sokoto ta Kudu, Aminu Tambuwal, ya ce zai marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar baya domin ya mulki Najeriya a kan Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Tambuwal ya ce Tinubu da ya sani a baya ya sauya daga zamanin da ya dan shi a baya lokacin fafutukar tabbatar da dimokradiyya.
Da yake jawabi a gidan Talabijin na Channels, tsohon gwamnan jihar Sokoto yace: “Idan Atiku yana takara da Bola Tinubu, ba zan goyi bayan Tinubu ba, Tambuwal ya kuma bayyana cewa ba zai koma jam’iyyar (APC) ba.
Dan majalisar ya bayyana cewa bai yarda da yadda APC ke mulkin Najeriya ba. “Ba zan koma APC ba, shawara ce ta kaina kuma ban yarda da yadda ake tafiyar da kasar a halin yanzu ba,” in ji shi.
