Ƙungiyar likitoci NARD ta umarci mambobinta da su shiga yajin aiki a faɗin ƙasar

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya NARD, ta sanar da shirin ta na tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani a duk faɗin ƙasar, a cikin makon sama.
Sabon shugaban ƙungiyar Mohammed Sulaiman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a wannan Lahadi, inda ya umarci mambobin ƙungiyar a duk faɗin Najeriya da su shirya domin fara yajin aikin daga ranar 1 ga watan Nuwamba mai zuwa.
A cewar Mohammed, sun ɗauki wannan mataki ne bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 30 da suka bai wa gwamnatin ƙasar, ba tare da ta waiwaye su ba.
Wannan mataki dai, na zuwa ne bayan cimma matsaya a taron ƙolin ƙungiyar da shugabanninta suka shafe sa’a biyar suna tattaunawa a ranar Asabar.
A baya dai, ƙungiyar ta bai wa gwamnatin ƙasar wa’adin kwanaki 30 don biya mata jerin buƙatun ta, da ta ɗauki alƙawari a baya, tare kuma da fito da wasu tsare-tsaren da za su bunƙasa walwalar mambobinta.
Dama dai, gabanin kwanaki 30 ɗin da ƙungiyar ta bayar, a lokuta mabambanta ta ba wa Gwamnatin Tarayyar Najeriya, wa’adi kafin ta shiga yajin aikin gargaɗi a ranar 12 ga watan Satumban da ya gabata.
