Yau ake zaɓen shugaban ƙasar Ivory Coast

0
1000245558
Spread the love

A yau Asabar al’ummar kasar Ivory Coast ke zaben shugaban kasa wanda ya raba kan kasar inda wasu ke son shugaba Alassane Ouattara ya yi tazarce, wasu kuma na ganin lokaci ne na samar da sabon shugabanci a kasar.

Fargaba ta karu sosai tun bayan cire manyan ‘yan takara biyu na jam’iyyun hamayya – wato tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da Tidjane Thiam, wani jigo a fagen siyasa kuma abokin kawancen Ouattara kafin ya zama abokin hamayya.

Wakiliyar BBC ta ce Shugaba Ouattara ya yi kira ga magoya bayansa su fito su zabe shi duk da yan kasar da dama na tunanin shi zai lashe zaben kafin zaben an samu rikici a sassan kasar da dama inda aka kama daruruwan mutane.

Alassane Ouattara mai shekara 83 yana takara ne domin neman mulkin kasar a zango na hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *