Hamas na yunƙurin kai hari kan fararen hula a Gaza – Amurka

0
1000232212
Spread the love

Amurka ta ce tana da abin da ta kira kwararan hujjoji cewa Hamas na shirin saba yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar kai hari kan fararen hula a Gaza.

Ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta ce idan har kungiyar ta ci gaba da kai harin, za a dauki mataki domin kare mutanen Gaza da kuma mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar.

Ana ta kai ruwa rana ne tsakanin ɓangarorin saboda gawarwakin da Hamas ta yi garkuwa da su da har zuwa yanzu ba ta gama miƙawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *