An rantsar da sabon shugaban Madagascar

0
1000228566
Spread the love

An rantsar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaban gwamnatin sojin Madagascar, bayan ya jagoranci hamɓarar da shugaba Andry Rajoelina.

An gudanar da bikin rantsar da sabon shugaban ne cikin gagarumin taro cike da murna da kaɗe-kaɗe, baya ga ɗaga takobi.

Tsohon shugaba Rajoelina wanda ‘yanmajalisar ƙasar suka tsige bayan tserewarsa waje a ƙarshen makon da ya gabata, ya yi Allah wadai da juyin mulki, kuma yaƙi amincewa da murabus duk da baya cikin ƙasar.

Rajoelina ya ce ya tsere daga ƙasar ne saboda dalilai na tsaro, yayin da babbar kotun Madagascar tuni ta tabbatar da sahihancin sabon shugabancin na soji, sa’o’i ƙalilan bayan juyin mulkin.

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres da Ƙungiyar Tarayyar Afrika AU, dukkanninsu sun yi watsi da juyin mulkin, wanda ke zuwa makonni bayan zanga-zangar matasa ‘yan Gen Z da ta ɓarke a ƙasar, sakamakon matsalar ƙarancin wutar lantarki da ruwan sha.

Yayin bikin rantsar dashi da aka gudanar a babbar kotun ƙasar, Randrianirina ya sha alwashin yin bakin ƙoƙarinsa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na shugaban Madagascar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *