Majalisar Dokokin Najeriya na son a yi zaɓen shugaban ƙasa a watan Nuwamban 2026

Majalisar Dokokin Najeriya ta bayar da shawarar sauya lokacin gudanar da zaɓen shugaban ƙasar zuwa watan Nuwamban 2026 maimakon Fabrairun 2027.
Shawarar na ƙunshe cikin daftarin ƙudurin dokar zaɓe ta 2025, da aka gabatar ranar Litinin a lokacin zaman sauraron jin ra’ayin jama’a na haɗin gwiwa tsakanin kwamitocin zaɓe na majalisun dokokin biyu da aka yi a Abuja.
Ƙudurin, ya nemi a sauya dokar zaɓe ta 2022 tare da amincewa da sabuwar dokar zaɓe ta 2025.
A cewar daftarin, ”za a gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa da na gwamnoni ƙasa da kwana 185 kafin ƙarewar wa’adin waɗanda ke riƙe da muƙaman”.
Ƴanmajalisar sun ce manufar sauyin shi ne tabbatar da kammala duka shari’o’in ƙorafe-ƙorafen zaɓe kafin ranar 29 ga watan Mayun 2027 da za a rantsar da shugaban ƙasa da gwamnoni.
