MSF ta yi gargaɗin ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki a arewacin Najeriya

Ƙungiyar Agajin Likitoci ta MSF ta yi gargaɗin samun ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki tsakanin ƙananan yara a arewacin Najeriya.
MSF ta ce a wannan shekara kaɗai ta duba ƙananan yara fiye da 300,000 aka samu da matsalar a jihohin yankin bakwai.
Ƙungiyar ta ce rashin abinci mai gina jiki na shafar lafiyar kwakwalen yara, lamarin hana su cimma wasu muhimman bangarori na ginuwar gaggar jikinsu.
Arewacin Najeriya ya shafe shekaru yana fama da rashin tsaro, lamarin da ya raba miliyoyin mutane da gidajensu tare da haifar da rashin noma.
