‘Shugaban Madagascar ya fice daga ƙasar’

0
1000218999
Spread the love

Rahotanni sun ce shugaban ƙasar Madagascar, Andry Rajoelina, ya fice daga ƙasar, sakamakon matsin lamba da ake yi masa na ya sauka daga mulki.

Matasan ƙasar sun ɗauki kwanaki suna zanga-zangar neman ya sauka daga mulki.

Kafofin yada labaran Faransa sun ce an fitar da shugaban daga ƙasar ne a cikin wani jirgin sojin Faransa a jiya Lahadi.

Yayin da suke cewa an fice da shi ne bayan amincewar shugaba Emmanuel Macron.

Hukumomin Faransa sun ce ba sa shisshigi a harkokin cikin gida na ƙasar .Ƴan adawa a majalisaer dokokin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa za su fara zaman tsige Mista Rajoelina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *