NELFUND ta sake buɗe sashen lamunin ɗalibai don neman tallafin shekarar 2024/2025

0
1000214110
Spread the love

Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya NELFUND, ya amince da sake bude shafin na karshe na tsawon sa’o’i 48 don baiwa manyan makarantu damar kammala aikin tantance dalibansu na yin hakan.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Abuja ranar Juma’a ta hannun Misis Oseyemi Oluwatuyi, Daraktar sadarwa na asusun.

Oluwatuyi ta ce za a fara amfani da shafin ne daga karfe 12:00 na safe ranar Lahadi, 12 ga watan Oktoba zuwa karfe 12:00 na safe a ranar Talata, 14 ga watan Oktoba.

Asusun NELFUND ta ce an tsawaita wa’adin ne domin a tabbatar da cewa an samu dukkan daliban da suka cancanta a cibiyoyin su yadda ya kamata tare da tantance su a wani bangare na shirin neman rancen NELFUND na shekarar 2024/2025 da ke gudana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *