Saura ƙiris Ghana ta samu gurbi a gasar Kofin Duniya

0
1000211369
Spread the love

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Ghana Black Stars na gab da samun gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan nasarar casa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya 5-0 ranar Laraba.

Mohammed Salisu, da Thomas Partey, da Alexander Djiku, da Jordan Ayew, da Kamaldeen Suleimana ne suka ci wa Ghana ƙwallayen a wasansu na Rukunin I.

Sakamakon ya sa Ghana ta haɗa maki 22 cikin wasa tara, kuma da zarar ta tashi wasan ƙarshe da Comoros ba tare da an doke ta ba za ta samu gurbin shiga gasar da ƙasashen Amurka da Mexico da Canada za su shirya.

Madagascar ce ta biyu a teburin da maki 19, sai Mali ta uku mai maki 15.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *