Majalisa Magabata a Najeriya ta amince da nadin sabon shugaban INEC

Majalisar magabata a Najeriya ta amince da nada Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga jihar Kogi da ke tsakiyar kasar a matsayin sabon shugaban hukumar zaben kasar.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce Shugaba Tinubu ne ya gabatar da sunan Farfesa Amupitan ga majalisar domin neman amincewarta.
Matakin na zuwa ne kwana uku bayan murabus din tsohon shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, wanda wa’adinsa ya kare.
Tinubu ya shaida wa majalisar cewa Farfesa Amupitan ne mutum na farko daga jihar Kogi da zai rike mukamin, kuma ba dan siyasa ba ne.
Nan take kuma duka mambobin majalisar suka amince da shi ba tare da sabani ba.
A yanzu shugaba Tinubu zai aika sunansa zuwa majalisar dattawan kasar domin amincewarta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Farfesa Amupitan, mai shekara 58, malami ne a Jami’ar Jos da ke jihar Plateau.
A 2014 ne ya samu mukamin babban lauya na SAN.
