Muna son a kafa kwamitin da zai zaɓi sabon shugaban INEC – Jam’iyyun siyasa

Jam’iyyun siyasa a Najeriya sun fara martani kan saukar shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Inec Farfesa Mahmood Yakubu daga mukaminsa bayan kawo karshen wa’adinsa na biyu
Kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyun Najeriya ya yi kiran samar da wani kwamitin da zai jagoranci nada sabon shugaban hukumar zaɓe ta Inec da kuma kwamishinoni.
A ranar Talata ne Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga muƙaminsa na shugaban hukumar zaɓen Najeriya tare da miƙa ragamar jagorancin Inec ga May Agbamuche kafin naɗa sabon shugaba.
Shugaban ƙasa ne kundin tsarin mulki ya ba damar zaɓen shugaban hukumar zaɓe bayan tuntubar majalisar ƙasa da ta ƙunshi tsoffin shugabanni da gwamnoni da shugabanannin majalisun tarayya.
