Shugaba Biya ya shafe mintina 25 yana jawabin yaƙin neman zaɓe

Kwanani biyar gabanin gudanar da zaɓen shugabancin ƙasar da za a yi ranar 12 ga wannan wata na Okotba, shugaban Kamaru Paul Biya ya fito bainar jama’a a wannan Talata inda ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa daga Moroua da ke Arewacin ƙasar.
Kafin wannan bayyanar, an jima ana raɗe-raɗin cewa shugaban ba ya da ƙoshin lafiya, yayin da wasu ke cewa ba ya da masaniya a game da batun tsayawarsa takara a wannan zaɓe, tare da cewa wasu muƙarrabansa ne ke amfani da sunansa domin cimma muradunsu na siyasa.
Paul Biya dai ya isa birnin Moroua a marecen Talata ne tare da rakiyar matarsa Chantal Biya, inda ya share tsawon mintuna 25 yana gabatar da jawabi a gaban ɗimbin magoya bayansa.
Kamar dai a 2018, ko a wannan karo Paul Biya ya zaɓi Moroua da ke kusurwar iyakar Kamaru, Chadi da Najeriya da ke matsayin babbar cibiyar da ke samar da ƙuri’u sama da milyaan 1 da dubu 200 domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa.
To sai dai raba-gari tsakaninsa da manyan ƴan siyasa na arewacin ƙasar da suka haɗa da Bello Bouba Maigari da kuma IssaTchiroma, na matsayin wani ƙalubale ga Biya a wannan karo.
