Tinubu ya buƙaci NAHCON ta rage kuɗin Hajjin bana

0
1000205955
Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin.

Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana.

Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na bana, ciki har da tattaunawa game da kuɗin kujera.

“Saboda yadda farashin naira ya haɓaka da kuma sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin Najeiya da aka fara gani, shi ne mataimakin shugaban ƙasa ya ce yana ganin idan har maniyyata sun biya tsakanin naira miliyan 8.5 zuwa miliyan 8.6 a bara, yanzu da darajar naira ta ɗaga, ya kamata a ga canjin da aka samu a kuɗin Hajjin bana.

“A nasa ɓangare, sakataren hukumar alhazan, Dr Mustapha Mohammad ya ce wannan matakin zai taimaka wajen ƙara yawan mahajjatan bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *